Kasashen Najeriya,China da India sun fiyawan Nakasassun yara a duniya – Bincike

0

Bincike ya nuna cewa kasashen Najeriya,China da India na cikin kasashen duniya da suka fi ywan yara da ke fama da nakasa a duniya.

Bayanai sun nuna cewa adadin yaran a wadannan kasashen ya kai miliyan 53.

An gudanar da wannan bincike ne a shekaran 2016 sannan gidauniyyar Bill da Melinda Gates ne suka samar da kudade da kayan aikin da aka yi amfani da su.

Ma’aikatan kiwon lafiya sun bayyana cewa nakasa matsala ce da kan kama yaro karami wanda kan hana shi girma kamar yadda sauran yaran da basu da nakasa.

Wadannan matsalolin sun hada da farfadiya, rashin kaifin kwakwalwa, shan inna, makanta, rashin ji da dai sauran su.

A Najeriya binciken ya nuna cewa a tsakanin shekarun 1990 zuwa 2016 yaran dake fama da wannan matsala sun karu daga miliyan 1.5 zuwa 2.5.

Sannan duk da hakan a tsakanin wadannan shekaru bincike ya nuna cewa an sami raguwar mace-macen yara kanana musamman ‘yan kasa da shekara biyar daga miliyan 3.4 zuwa 2.7 a kasashen kudu da Saharan Afrika.

Bayan haka wani jami’ar cibiyar ‘Global Research on Developmental Disabilities Collaborators (GRDDC) Bolajoko Olusanya ya bayyana cewa adadin yawan yaran dake fama da wannan matsalar musamman a Najeriya na bashi takaici musamman yadda wadannan yara kan yi fama da rashin kula duk da matsalar da suke fama da.

Olusanyan ya ce talauci na daga cikin babban matsalar da ke ci wa iyayen wadannan yara tuwo a kwarya sannan ya kara da cewa wayar wa iyaye kai game da haka, farshin samun kula a asibitoci da samun taimako zai taimaka wajen kawo karshen wannan matsala.

A karshe Olusanyan yace gwamnati za ta hannu da UNICEF, WHO da babban bankin duniya domin samun bayanai kan hanyoyin guje wa wannan matsalar da yadda ya kamata a kula da wadannan yara.

Share.

game da Author