Majalisa ta kafa kwamiti don binciken shigowar kwayoyi daga Kasar China

0

Majalisar dokoki ta kasa ta kafa kwamiti domin binciko ko kwayoyin da kasar China ke sarrafawa da naman mutattun mutane sun fara shigowa kasar nan.

Majalisar ta amince kan haka ne bayan Johnson Agbonayinma mai wakiltan jihar Edo na jam’iyyar APC ya yi wannan maganar a zauren majalisar.

Agbonnayinma ya kara da yin kira ga majalisar da ta gaggauta daukan mataki akan wannan matsala ganin cewa idan har aka bari mutane suka fara amafani da shi zai iya illata lafiyar su.

A karshe majalisar ta amince ta gaiyaci hukumar (NAFDAC) da hukumar lekan asiri na kasa (NIA) domin yi mata bayani kan wadannan kwayoyi.

Idan ba manta ba a makon da ta gabata ne hukumar kula da ingancin kaya na kasa (SON) ta bayyana cewa za ta sa ido don ganin ta hana shigowa da wasu kwayoyin da kasar Sin ke sarrafa su da jikin matattun mutane a Najeriya

Jam’in hukumar Bola Fashina ya fadi haka inda ya bayyana cewa hukumar su ta sami labarin haka ne a wata wasika da aka aiko mata, hukumar Kwastam da NAFDAC.

Fahina ya ce wasikar ta bayyana yadda kasar Sin ke sarrafa wasu kwayoyin magunguna da naman jikin mutanen da suka mutu a dalilin kamuwa da cututtuka kamar su kanjamau, Hepatits sa sauran su.

Wasikar ta bayyana cewa amfani da wadannan kwayoyi na cutar da lafiyar mutum ganin cewa mutum zai iya kamuwa da wadannan cututtuka da ya yi ajalin wadannan mutane.

Fashina yace za su kara zage damtse don ganin sun hana wadannan magunguna shigowa kasar duk da cewa wannan aiki na hukumomin NAFDAC ne da Kwastam.

Bayanai sun nuna cewa arewa maso gabashin kasar Sin ne ke sarrafa wadannan kwayoyi.

Share.

game da Author