Garin cire ciki mai siyar da magani ya kashe mata a Barno

0

A ranar Lahadi ne rundunar ‘yan sandan jihar Barno ta damki wani mai shagon siyar da magani mai suna Muhammad Isa da zargin kashe wata mata mai ciki a gidan sa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Damian Chuckwu ya sanar da haka wa manema labarai a Maiduguri.

Chuckwu ya bayyana cewa Isa mai shekaru 32 ya aikata haka ne a kokarin zubar wa wata matashiya ciki.

” Da Isa ya yi mata allura sai ta tafi gida amma washe gari sai ta sake dawo wa cewa wannan allura da ya yi mata bai yi aiki ba.

” Daga nan sai ya kaita gidan sa inda ya kara yi mata wasu allurai sannan ya saka mata ledan ruwa. Hakan na faruwa kuwa sai wannan yarinya ta ce ga garin ku nan.

Chuckwu ya ce Isa ya nemi taimakon abokin sa domin boye gawar yarinyar amma abokin ya kai karan sa ga jami’an tsaro.

‘‘Mun gano cewa Isa bashi da horo irin na ma’aikatan kiwon lafiya sannan wannan ba shine karo na farko ba da yake aikata hakan a shagon sa.

A karshe yace Isa na nan tsare a ofishin ‘yan sandan sannan za a gurfanar da shi a kotu bayan sun kammala bincike.

Share.

game da Author