Sufeto Janar din ‘yan sandan Najeriya ya sanar cewa an aika da dakarun tsaro na ko ta kwana zuwa Kaduna a dalilin barkewar tarzoma da aka samu a wasu sassan jihar.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne wasu hasalallun matasa suka far wa kasuwar magani inda mutane sama da 50 suka rasa rayukan su sannan a ka bannata dukiya masu dimbin yawa.
Gwamnatin Kaduna ta sanar kafa dokar hana walwala a wannan gari na Kasuwan Magani.
Wannan kisa bai yi wa wasu da dama dadi ba inda sanadiyyar haka matasa suka tattare manya-manyan titunan jihar suka fara aikata dabanci.
Gwamnatin jihar ta sanar da saka dokar hana walwala na awa 24 a cikin garin Kaduna da kewaye.