ANNOBAR FARIN DANGO: Helikwafta zai yi wa gonakin shinkafar Kebbi feshin maganin kwari

0

Biyo bayan barkewar mamayar farin dango a gonakin shinkafa a Jihar Kebbi, gwamnatin jihar ta bayyana cewa za ta yi amfani da jiragenn helikwafta domin yin feshin maganin kwari a gonakin da farin suka mamaye.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya ruwaito cewa gonakin da farin suka mamaye su na cikin karamar hukumar Ambursa ne, da ke kusa da Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Kakakin Gwamnan Jihar mai suna Abubakar Dakin gari, ya ce za a fara feshin nan da kwanaki biyu, wato Laraba kenan.
Ya ci gaba da cewa gwamnati za ta ci gaba da goyon baya da tallafi ga manoma domin jihar ta ci gaba da rike kambunta na wadda ke sahun gaba a fannin noman shinkafa.

Wasu gungun manoma ne a karkashin wani mai suna Shehu Maigishiri, suka yi wa gwamnatin jiha kururuwar neman daukin gaggawar kakkabe musu farin dangon da suka mamaye musu gonakin shinkafa.

Share.

game da Author