Fiye da rabin fursunonin da ke jiran hukunci ‘yan kasa da shekaru 30 ne -Inji Kungiya

0

Sama da kashi 50 bisa 100 na fursunonin da ke tsare a kurkuku masu jiran a yanke musu hukunci, ‘yan kasa da shekaru 30 ne.

Wata kungiyar masu karatun aikin Lauya da Shari’a a Jami’o’in kasar nan ce mai suna NULAI ta bayyana haka.

Ta kuma kara da cewa gaba dayan masu jiran a yanke musu hukunci, sun zarce kashi 70 bisa 100 na daurarrun da ke gidajen yarin cikin Najeriya.

Najeriya na da fursunoni 75, 589, daga cikin su 24, 450 ne kadai aka yanke wa hukunci. Sauran 51,139 kuwa duk su na jiran a yanke musu hukunci ne.

Haka wannan kungiya ta bayyana a wani taron kara wa junan kungiyar sani da aka shirya a Abuja, ciki har da kai ziyara a kurkukun Abuja.

Jami’ar tantance adadin daurarru ta kungiya mai suna Charissa Hassan, ta ce abinda ke haifar da yawan matasa ‘yan kasa da shekaru 30 a gidajen kurkuku, ta ce matasan da ba su da kudi, kuma bas u da mai tsaya musu, su ne suka fi dadewa tsare a gidajen kurkuku.

Charissa ta kara da cewa a kan naira dubu hudu ko dubu biyar sai matashi ya yi shekaru ya na tsare, tunda ba shi da mai biya masa tarar.

Share.

game da Author