Darakatan Ofishin Binciken Sahihancin Ababen Hawa (VIO), na Jihar Filato, John Dayah, ya bayyana cewa jami’an sa sun kwace Keke-NAPEP sama da 800, saboda kin bin umarnin yi musu rajista da musu baburan suka ki yi.
Dayah ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai, NAN a Jos, cewa za a bai wa duk wanda ya cika umarnin yi wa babur din sa rajista.
“Za mu ba su uzirin su zo su yi wa baburan su duk wata rajistar da ta cancanta ko ta wajaba su yi musu, kafin a bar su su dauki abin su.
Ya ce an girka jami’an VIO a cikin Jos da Bukuru domin su kama duk wani babur din Keke-NAPEP wanda ba shi da rajista.
Ya ce yawancin baburan duk an damka su ga masu su, bayan zun je da kan su sun yi musu rajista.
Discussion about this post