An gurfanar da Nura da ya dare tsanin wayan tarho a kotu a Abuja

0

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta gurfanar da wasu maza uku a kotun dake Wuse zone 2 a Abuja bisa zargin cewa wadannan mutane sun yi kokarin kashe kan su wanda yin haka laifi ne.

An zargi Iliyasu Lawal mai shekaru 28, Nura Iliyasu mai shekaru 29 da Idris Suleiman mai shekaru 28 da laifin tada fitina ne da hankulan mazauna garin Abuja.

Idan ba a manta ba a ranar 12 ga watan Satumba Nura Iliyasu ya dare kololuwar tsanin na’urar wayar tafi da gidan ka wanda ke kusa da fadar shugaban kasa don nuna fushin sa ga durkushewar tattalin arzikin Nageriya.

Iliyasu ya bayyana cewa zai zauna a kan wannan tsani na kwanaki bakwai sannan ba zai damu ba koda zai rasa ran sa ne.

” Koma bayan tattalin arzikin da muke fama da shi a kasar nan ya hana mutane sakat. An wayi gari mutane da dama basu iya ci abinci saboda talauci, rashin aikin yi, rashin samun ababen more rayuwa da sauran su.

” Burina za ta cika idan har na mutu a nan idan dai hakan zai kawo canji a kasar nan.

Lauyan da ya shigar da karan Augustine Urom ya bayyana cewa ashe Iliyasu ya aikata haka ne da taimakon abokan sa biyu.

Alkalin kotun Muhammad Abdulmumini ya bada belin su akan Naira 250,000 sannan kowanen su zai gabatar wa kotun da shaida daya ya kai matakin girma na bakwai a aikin gwamnati.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 16 ga watan Oktoba.

Share.

game da Author