‘Yan bindiga sun sace mutane 16 a Kaduna

0

Masu garkuwa dauke da bindigogi sun yi garkuwa da wasu masu hakar ma’adinai a karamar Hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna.

Rundunar ‘yan sanda Kaduna ne ta sanar da haka sannan ta kara da cewa wadannan masu garkuwa sun tare mutanen ne a daidai suna komawa gida daga wurin aikin su na hakar ma’adinai.

Kakakin rundunar ya kara da cewa cikin wadanda aka sace akwai wani mai suna Tanimu Isah.

” Tuni dai jami’an mu sun sun fantsama cikin daji domin bin sawun wadannan masu garkuwa. Sannan kuma mun sami rahoton cewa sun fara yi wa ‘yan uwan wadanda suka sace din waya don a biya kudin fansa.”

Share.

game da Author