Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi barazanar cewa a saurari bi-ta-da-kullin da zai yi wa jam’iyyar PDP, matsawar aka bada bori a kan wasu ‘yan takarar da jam’iyyar APC ta turo a cikin jam’iyyar, har aka fasa taron gangamin jam’iyyar a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Ya kara da cewa jihar sa ba za ta zabi duk wani dan takarar da ke neman shugabanci ido-rufe ba, wanda ke yaki da tattalin arzikin jihar sa, ta hanyar kin amincewa da gudanar da gangamin APC na kasa a Fatakwal ba.
Wike ya yin wannan gargadin ne ya na mai kara cewa Jihar Ribas za ta sabule wa PDP zani a tsakiyar kasuwa, idan aka bari wasu masu takarar shugabancin kasa a jam’iyyar, wadanda ya yi amanna cewa jam’iyyar APC ce ta turo su, suke yi wa PDP kura-da-fatar-tinkiya suka kawo wa taron PDP cikas.
Da ya ke magana a wurin taron karbar bakuncin Gwamna Ibrahim Dankwambo, wanda ya kai ziyarar neman goyon baya a zaben fidda-gwamnin PDP, Wike ya ce ba wani dan takarar shugaban kasa da zai ki amincewa a gudanar da taro a Fatakwal.
Ya kuma kara da cewa duk wani dan takarar shugaban kasa da ke adawa da gudanar da taro a Jihar Rivers, to ya manta da batun samun goyon baya daga wakilan jihar Ribas din.
“Kai bari na fito na fada kowa ya ji, duk wanda ya kuskura tsone wa jihar Ribas idanu, to za mu sabule wa PDP zani a kasuwa nan take. Ba fa wanda ya isa ya zo ya ci arzikin jihar Ribas, sannan kuma ya yi mana dariya, kuma a zauna lafiya.
“Ba wani dan takarar shugaban kasa da ya isa ya ci amfanin mu sannan kuma ya yi watsi da mu, ya juya mana baya. Ba roko ko magiya muka yi mu ka nemi alfarmar a gudanar da taron nan a jihar Rivers ba. Amma mun tabbata yin taron zai habbaka tattalin arziki jihar, saboda jama’a za su samu kudi sosai.
“ Duk masu adawa kan yadda jihar Ribas za ta samu kudi idan an gudanar da zaben a nan jihar, to ba za mu goya masa baya ba.”
Ya ce ko a yi taron a Jigawa ko Adamawa, ko ma ina ne dai, sai wanda ya yi nasara ya bayyana a ranar.
“Ban san dalilin da ya sa mai neman takarar shugabancin kasa kuma ya zo ya buge ya na tsoron duk ma inda za a yi taron gangamin zaben fidda-gwani ba.
“Ba wanda ya isa ya raina mana hankali. Iya-shegen ya fa isa haka nan. PDP ta san cewa mu jujin da za a rika jibga wa kowace shara ba ne. Mu fa ba mutanen da za a ci moriyar gangar su sannan a jefar da kwauren ta, kuma su yi shiru ba ne.
“Kai mu fa ba karuwai ba ne, da kowane jarababbe zai zo ya biya bukatar sa, sannan ya sa wandon sa ya yi gaba…..”
“Za mu rama a lokacin da ramuwar-gayya ta fi gayya ciwo. Idan ka koma ka fada wa sauran abokan takarar ka cewa ba mu da sha’awar shirya taron gangamin jam’iyya. Amma tunda aka rigaya aka ba mu, har mun yi shirye-shirye, karya mutum ya ke ya ce kuma zai zo mana da wani zance daban. Bai isa ba, ko wane ne.” Inji Gwamna Wike.
Wike ya ce akwai wasu ‘yan takarar da kowa ma ya san cewa in dai batun neman takarar shugabancin kasar nan ne, to wutsiyar rakumi fa ta yi nesa da kasa. Amma don rainin hankali sun sayi fom don kawai sun ga an mika takarar a Arewa.
Ya nuna cewa ya na mamaki don rashin kunya dan takarar shugaban kasa ya ce bai gamsu da yin gangamin zaben fidda gwani ba a jihar Ribas, amma kuma ya na matukar son kudin man fetur din da ake hakowa daga jihar Ribas.
Wike ya ce ta ya za a yi mutum ya je kamfen jihar Ribas, ya yi musu alkawarin zai sake fasalin kasa idan ya ci zabe. Sai bayan ya koma yankin su ya koma ya na sukar jihar Rivers kuma? Ya de shin idan wannan mutumin ya zama shugaban kasa me zai faru kuma?
A kara da shan alwashin cewa lokaci ya kusa da zai tona asirin ‘yan takarar shugabancin kasa da APC ta turo cikin PDP domin su yi wa PDP din kafar-ungulu tun a zaben fidda-gwani.
Daga nan ya bayyana cewa Dankwambo ya cancanci zama shugaban kasa, kuma jihar sa za ta goya masa baya a lokacin da wakilan zabe suka taru domin daukar dan takarar da za su goyi baya a zaben fidda-gwanin jam’iyyar.
Discussion about this post