AMBALIYA: NEMA ta karbi naira biliyan uku domin kai daukin gaggawa

0

Hukumar Ajajin Gaggawa, NEMA ta karbi naira biliyan uku daga hannun gwamnatin tarayya domin kai daukin gaggawa a inda aka fara samun ambaliya, da kuma fito da hanyoyin rage barnar ambaliyar.

Wannan kudade da aka ba hukumar, sun biyo bayan wani kakkausan gargadi ne da Hukumar Kula da Sauyin Yanayi na ti a ranar 7 Ga Satumba, cewa akwai alamun barkewar ambaliya a jihohin kasar nan da dama.

Shugaban NEMA Mustapha Maihaja ne ya bayyana karbar kudaden daga hannun gwamnati, a wajen wani taron manyan jami’an hukumar da kuma masu ruwa da tsaki a kan ambaliyar cewa an bayar da kudin ne domin a yi shiri na gaggawa.

Ya kara da cewa sannan za a gaggauta kai agaji tare kuma da samo hanyoyin da za a kauce ko a rage mummunar barnar ambaliyar.

Sai dai kuma ya ce wani abin damuwa da rahotonnin da kwamiti ya kai wa hukumar shi ne tuni har ambaliyar ta fara barna a jihohin Neja, Kogi, Delta da Anambra.

Idan ba a manta ba, ranar Juma’a Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Maihaja ya kaddamar da dokar-ta-baci a kan ambaliya a fadin kasar nan.

Cikin makonni biyu da suka gabata, jihohi da dama sun hadu da ibtila’in ambaliyar da ta janyo asarar rayuka da dimbim dukiyoyi.

Share.

game da Author