Wani tsoho mai shekaru 74 dan asalin kasar Pakistani ya rasu a garin Maka bayan kammala aikin hajjin sa.
Wannan tsoho sai da yayi shekaru 43 yana tara kudi don ya tafi kasa mai tsarki don ya yi aikin hajji.
Shafin HajjReporters ne ta ruwaito wannan labari in da ta kara da cewa an sami wannan tsoho ne kwance kamar yana hutawa ashe Allah ya dauki abin sa a garin Makka.
Tuni dai har an yi jana’izan sa a nan Makka.
Allah ya ji kan sa. Amin.
Discussion about this post