Wata Kotun Majistare da ke Abuja, Babban Birnin Tarayya, ta kori karar da gwamnati ta shigar kan Jones Abiri, tare da cewa tsarewar ma da aka yi masa har na tsawon shekaru biyu ba tare da kai shi kotu ba, babban laifi ne mai muni kwarai.
Korar wannan kara dai ta biyo bayan shigar da wani roko da lauyan Abiri yay i mai suna Samuel Ogala, inda ya nemi a maida shari’ar Abiri a jihar Bayelsa, tunda a can ne aka ce ya aikata laifin da ake zarge shi da aikatawa.
Idan ba a manta ba, cikin makon da ya gabata ne Kotun Tarayya a Abuja ta bada umarnin gwamnati ta biya shi diyyar Naira Miliyan 10 saboda tsare shi da aka yi ba bisa ka’ida ba.
Hakan ya biyo bayan karar da ya shigar bayan an bayar da belin sa a ranar 15 Ga Agusta.
Discussion about this post