Akwai damuwa matuka game da tulin bashin da Najeriya ta ciwo – Amina

0

Tsohuwar Ministar Muhalli ta Shugaba Muhammadu Buhari, kuma wadda a yanzu ita ce Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta nuna matukar damuwar ta da irin tulin bashin da ake bin Najeriya da kasashen Afrika.

Amina ta yi wannan jawabi ne a wani taron masana da Bankin Bada Lamuni na duniya (IMF) ya shirya, kuma aka nuna bidiyon na jawabin na ta a shafin intanet na IMF din.

Amina ta nuna takaicin yadda Najeriya ta sake riftawa cikin ramin tulin bashin da ke neman hadiye ta, duk kuwa da cewa tsohuwar ministar harkokin kudade, Ngozi Okonjo-Iweala ta tsamo Najeriya daga cikin bashin da ya hadiye ta a cikin 2005.

Ta nuna cewa kamata ya yi cibiyoyin kudade da kuma kasashe masu tasowa su rika zaman tattauna makomar tattalin arzikin su tukunna tare ma da yin duba da hanyoyin da kasashen za su rika kirkirar hanyar samun arzikin da zai inganta tattallin su.

“Daidai lokacin da na ke baro birnin New York domin halartar wannan taron, damuwar da mu ka nuna a wani zaman taron da mu ka yi a China da kuma rahotannin da ke a gaban mu, to maganar gaskiya fa tulin basussukan nan ya yi yawa.

“Bisa la’akari da irin namijin korarin da Ngozi ta yi wajen kokarin da ta nuna aka yafe tulin basussuka a baya, to a yanzu kuma mun sake riftawa cikin wani ramin tulin bashi iyar wuya. Wannan kuma abin damuwa ne matuka.”

Amina ta bayyana wa Shugaban Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), Christine Lagarde cewa irin tunani ko fahimtar da shugabannin Afrika ke wa ma’anar cigaba abin damuwa ne ainun.

Ta ce ya kamata a rika yin zaman nuna wa Afrika hakikanin hanyoyin da ake bi a samu ci gaba a kasashe masu tasowa, tare da tabbatar da cewa an dan taka wa bayar da bashin burki haka nan.

Cikin 2005 ne a zamanin gwamnatin Olusegun Obasanjo, Najeriya da wata kungiyar kasashen da ke bada lamuni da aka fi sani da Paris Club suka cimma yarjejeniyar yafe wa Najeriya bashin dala bilyan 30.

Wannan kokari ne wanda kacokan ministar harkokin kudade ta lokacin, Ngozi ce ta yi shi.

Share.

game da Author