Wasu shugabanni masu fada a ji daga yankunan kudancin Najeriya da ya hada da Yankin ‘yan Kabilar ‘Yarbawa wato Kudu Maso Yamma Kudu Maso Kudu da kuma yankin Arewa ta Tsakiya, sun yi tir ga Shugaba Muhammadu Buhari saboda cire shugaban hukumar tsaro ta SSS, Mathew Seiyefa da ya yi, ya maye gurbin sa da dan Arewa.
Shugabannin sun ce cire Seiyifa dan kudu da aka yi, bayan an nada shi shugabancin riko kwanan nan, maimakon a jaddada masa shugabancin, ya nuna kenan Buhari bai yi amanna da dunkulalliyar Najeriya ba, inda ake son shugaba ya rika gudanar da ayyukan sa a bisa adalci ba nuna bangaranci ba.
An cire Seiyifa jiya Alhamis, aka maye gurbin sa da Yusuf Bichi, wanda zai karbi ragamar jagoranci a yau Juma’a.
Seiyefa dan yankin Neja-Delta ne, kuma cire shi bai yi wa wadannan shugabanni dadi ba, inda suka fitar da takardar manema labarai cewa Buhari ya fi fifita bangaranci fiye da kishin kasa a nade-naden mukaman shugabannin hukumomin tsaro da ya ke yi.
Yayin da nada Seiyifa da Osinbajo ya yi, ya samu jinjina da goyon baya daga jama’a da kuma masu rajin kare hakkin jama’a, ganin yadda Lawal Daura ya rika yin mulkin kama-karya a hukumar SSS, cire Seiyifa kuma watanni biyu bayan nada shi ya haifar da suka ga Buhari.
Na farko dai sai cikin shekara mai zuwa ne Seiyifa zai yi ritaya, na biyu kuma an maye gurbin sa da dan Arewa. Na uku kuma a na garin shugabannin hukumomin tsaron kasar nan 12 daga cikin 15 da ake da su, duk ‘yan Arewa ne yanzu a zamanin mulki Buhari, ba kamar yadda sauran shugabannin kasa da suka shude suka gudanar da na su mullkin ba.
Dama kuma PREMIUM TIMES ta buga wani labari da ya tabbatar da yadda Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari ya rika yi wa Seiyifa katsalandan, jim kadan bayan da Osinbajo ya nada shi.
Ann ruwaito yadda ya rika soke wasu nade-nade da Seiyifa ya yi a hukumar tsaro ta SSS.
Wasu na cewa cire Seiyifa na da nasaba ne da zaben 2019, domin Buhari ya yi hakan ne da zimmar nada wanda zai fi amincewa da shi rike shugabancin hukumar SSS a lokacin zaben 2019.
Sun ce idan ba haka ba, me ya sa za a cire Seiyifa, wanda bai dade da nadawa ba, kuma sai shekara mai zuwa ne sannan wa’adin ritayar sa zai cika?
Yanzu dai ba a san yadda za ta karke ba a yau Juma’a, bayan da Seiyifa ya bada ikon SSS ga hannun Yusuf Bichi. Shin ritayar dole za a yi masa duk kuwa da cewa lokacin yin ritayar sa bai yi ba, ko kuwa mukamin sa na baya zai koma, duk kuwa da cewa shi ne mafi girma a hukumar ta SSS?
Shugabannin da suka la’anci sauke Seiyifa da kuma nada Bichi dai sun ce tun da Buhari ya hau sai kokarin kashe Najeriya da kuma wargaza ta a matsayin dunkulalliyar kasa ya ke yi, ta hanyar nade-naden ‘yan Arewa da ya ke yi a manyan mukamai, musamman na tsaro.
Sun bada hujjar cewa akwai ‘yan kudu har mutane hudu a cikin SSS wadanda ke gaba da Yusuf Bichi, kuma a cikin su ne ya kamata a dauka, idan har canja Seiyifa ya zama tilas. Sun kuma ce kamata ya yi a bar Seiyifa ya ci gaba har ya yi ritaya a shekara mai zuwa.
Wadanda suka sa hannu a kan takardar bayan taron da shugabannin suka gudanar, sun hada da:
Cif E.K Clark daga Kudu maso Kudu, Cif Ayo Adebanjo daga Kudu maso Yamma, Cif John Nwodo daga Kudu maso Gabas da kuma Mista Bitrus Pogu daga Yankin ‘Middle Belt’, yankin da aka fi sani da Arewa ta Tsakiya.