Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Katsina (SEMA) Haruna Musa ya bayyana cewa a bana ambaliyar ruwa ta rusa gidaje 4,000 a jihar.
Musa ya fadi wa manema labarai haka ne a garin Katsina ranar Alhamis inda ya kara da cewa kananan hukumomin da ambaliyar ya fi shafa sun hada da Baure, Daura, Jibiya, Malumfashi, Kusada da Musawa.
” Binciken da muka gudanar ya nuna cewa mutane biyu sun rasa rayukan su bayan gida ya rushe a kansu, da dama sun sami rauni sannan gidaje da dama sun rushe a dalilin ambaliyar ruwan bana.
Ya kuma kara da cewa a duk mako hukumar su kan saurari koke-koken aukuwar ambaliyar ruwa a sassan jihar.
A dalilin haka ne shugaban hukumar da ke kula da shiyyar arewa maso yamma Ishaya Isah yace hukumar sa ta zauna da masu fada a ji na hukumar domin samar da yadda za a gujewa aukuwar haka nan gaba.