Gwamnan jihar Nasarawa Tanko Almakura ya roki malaman almajiran jihar da su dai kyale yaran da ke karatu karkashin su galantoyi a titunan jihar.
Almakura ya bayyana haka ne da yake rantsar da sabbin malamai 2000 firamare da jihar ta dauka.
Almakura ya ce gwamnati za ta iya dan yi wa malaman ihisani domin su daina kyale yaran na gararamba a titunan jihar.
Ya ce a yanzu dai gwamnati ba zata hana yaran wannan galantoyi ba amma lallai za ta dau mataki akai don ganin sun daina wannan yawace-yawace a titunan jihar.
” Nan ba da daewa ba gwamnati zata fara amfani da makarantun da aka gina domin karatun almajiranci a jihar.
” Sannan zamu gana da malaman wadannan yara domin tsaro hanyoyin da za a bi don hana yaran wannan yawon barace-barace.