Gwamnatin Tarayya ta amince da kashe naira bilyan 1.3 domin gudanar da wasu manyan ayyuka har guda biyar a masu muhimmanci a kasar nan.
Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana haka jiya Lahadi a yayin da aka hira da shi a matsayin babban bako a Gidan Talbi na kasa, NTA a Abuja.
Ayyukan guda biyar da ministan ya bayyana za a kashe makudan kudaden a kan su, sun hada da aikin titin Lagos zuwa Ibadan, aikin ginin Gadar Neja ta biyu da kuma aikin gina titin da zai hade yankin Kudu da Gabas na kasar nan.
Sauran ayyukan sun hada aikin hanyar Abuja zuwa Kano da kuma aikin tashar wutar lantarki ta Mambilla.
Ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta dau aniyar inganta rayuwa ta hanyar raya karkara da ayyukan raya kasa, a fadin kasar nan tare da farfado da ayyukan da gwamnatin baya ta watsar ba ta karasa ba.