Jami’ar Hukumar Kula da Ingancin kayayyaki ta Kasa, SON Bola Fashina ta bayyana cewa hukumar ta gano wasu rigunar makarantan yara dake kawo cutar Sankara.
Fashina ta ce binciken da suka gudanar ya tabbatar musu cewa wasu sabin kayan makarantan yara da wasu kamfanoni biyu suka sarrafa a kasar Sin na sa mutum kamuwa da cutar daji.
Ta ce bincike ya nuna cewa kamfanonin Sing Shun Fat School-Clothier da Zenith Uniform na cika yawan sinadarin 4-amino wajen rina kaya wanda a dalilin haka ne ke sa mutane kamuwa da cutar sankara a jiki.
Bayanai sun nuna cewa kasashen duniya da dama sun gano illar da wannan sinadarin ke da shi inda hakan ya sa suka hana amfani da shi wajen rina kaya a kasashen su.
Fashina ta ce a dalilin haka ne suke kira ga mutane da su guji amfani da irin wadannan kayayyaki su kuma kai karan duk wanda suka ga yana amfani da irin wadannan kaya.
Discussion about this post