Majalisar Dinkin Duniya, UN, ta bayyana cewa a cikin 2017 an kashe ma’aikatan jinkai na majalisar har 139 a kasashe daban-daban.
Har ila yau, ta kara da cewa an kuma ji wa 102 raunuka, yayin da aka yi garkuwa da 72.
Daga nan sai ta yi kiran da a rika kare lafiya da rayuwar ma’aikatan jinkai a duk inda suka a duniya.
Babban mai kula da raba agajin gaggawa na UN, Mark Lowcock ne ya bayyana haka a lokacin da ake taron tunawa da masu ayyukan jinkai da suka rayukan su a wuraren da ake yaye-yake a duniya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 19 Ga Agusta, 2018 ta zama Ranar Ma’aikatan Jinkai ta Duniya, a kara nuna wa duniya muhimmancin aikin da suke yi, da kuma irin yadda su ke sadaukar da rayuwar su.
Ya ce wannan ne karo na biyar a duk shekara, har sau biyar a jere da ake kashe ma’aikatan jinkai sama da 100 a duk shekara.
Majalisar ta ce wadanda suka rasa rayukan su cikin 2017 sun yi yawa, tun bayan da aka kashe mutum 156 cikin 2013.