Hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta jihar Jigawa (JPHCDA) ta raba wa mutane 93,101 gidajen sauro a karamar hukumar Hadejia.
Jami’in hukumar Yusuf Bashir ya fadi haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis a Hadejia.
” Mun bi gida-gida muna raba wa mutane katin karban gidajen sauro domin kare su daga kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro.
A karshe ya mika godiyar sa ga karamar hukumar Hadejia kan mara musu bayan da suka yi a lokacin da suka zo wayar da kan mutanen garin game da mahimmancin amfani da gidan sauro.
” Goyan bayan da kuka bamu ya taimaka mana wurin ceto rayukan mutane da dama daga kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro a Hadejia.”