A yau Juma’a ne wani gini dake Unguwar Jabi a Abuja ya rufta kan mutane.
Wata mata da abin ya auku a Idanu ta ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ginin ya rufto ne haka kawai.
” Ina tsaye a can kawai sai muka ga gini ya rufto kasa. Mutane biyu sun rasu sannan akwai yiwuwar ginin ya danne wasu.
A yanzu dai ma’aikatan bada agaji na gaggawa na wannan wuri ana ta hako ginin ko za a samu wasu a ciki.
Bayan haka, Mukaddashin shugaban kasa ya zaiyarci wannan wuri domin gani wa kan sa abin da ya faru.

