A yau Litini ne jam’in yada labarai na rundunar sojin Najeriya Texas Chukwu ya bayyana cewa dakarun rundunar ‘Operation yaki’ dake aiki a garin Kukawa a karamar hukumar Baga jihar Barno sin harbe wasu ‘yan Boko Haram uku.
Chukwu ya fadi haka ne da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri inda ya ce an fafata ne a kauyen Kalamari dake kusa da Kukawa.
” Dakarun sun iske Boko Haram din na sata ne a kauyen. Dakarun mu sun sami nasarar harbe uku daga cikin su sannan sun kwato bindigogi da dama.