Masu cewa na hada kai da Lawal Daura sun raina muku hankali -Saraki

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya karyata masu zargin cewa ya hada kai da Lawal Daura jami’an SSS suka mamaye majalisa a jiya Talata.

Jam’iyyar APC ce ta yi wannan zargin a yau Laraba, bayan da a jiya Talata ta yi tir da mamaye majalisar da SSS suka yi, wanda hakan ne ya sa aka tsige Daura daga kan mukamin sa.

Saraki ya yi wannan raddin ne a taron manema labarai da ya gabatar a yau Laraba a Majalisar Dattawa.

“Bai kamata mu raina wa ‘yan Najeriya hankali ba.” Inji Saraki, ya kara da cewa shi ma ai jami’an tsaro sun sha gasa masa aya a kai, ciki har da Lawal Daura din da ake magana.

Daga nan sai ya kara kafa hujja da cewa ai shi ma har rage masa jami’an tsaro an yi, kamar yadda aka yi wa Kakakin Majlaisar Tarayya, Yakubu Dogara, ba tare da bin ka’idojin da doka ta shimfida ba.

Share.

game da Author