Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato Terna Tyopev ya bayyana cewa sun kama wasu ‘yan Sarasuka 33 a titin Bauchi dake karamar hukumar Jos ta Arewa, jihar Filato.
Ya fadi haka ne da yake hira da PREMIUM TIMES ta wayar tarho ranar Talata.
” Wannan tashin haka ne ya faro daga unguwar Nasarawan Gwom tsakanin ‘yan kungiyoyin ‘yan daba da basa ga maciji da juna. Daga nan ne fa suka kaure in da har wasu da basuji ba basu gani ba suka sami raunuka a jikkunansu a wannan tashin hankali.
” Sannan sun farfasa motocin mutane, da shaguna bayan sare sare da suka yi.
Tyopev ya ce bayan yan dabar 33 da suka kama, sun kwace makamai da dama daga hannun su sannan kuma sun kwato kwalayen tramadol daga hannun mutanen.
Yanzu dai komai ya lafa saidai matafiya titin Jos zuwa Bauchi sun dan dauke kafa.
Discussion about this post