Sai fa Najeriya ta ciwo bashi za ta iya yi wa jama’a ayyuka

0

Babbar Daraktar Kula da Hada-hadar Basusussuka ta Kasa, Patiencwe Oniha, ta bayyana cewa babu wata makawa idan dai har ana so a yi aiki da kasafin kudi na 2018, to tilas sai Najeriya ta ciwo bashi sannan za ta iya yin manyan ayyukan da aka wa jama’a alkawari.

Oniha ta yi wannan bayanin a wani taron da aka gudanar dangane da Hukumar Bada Lamuni ta Duniya (IMF).

A wurin taron dai an tattauna yadda za a rika kirkiro hanyoyin samun kudin shiga na cikin gida Najeriya da kuma batun zuba jari daga ‘yan kasuwa masu zaman kansu.

A cewar ta, kudaden rarar ajiyar da Najeriya ke tutiya da su da kuma danyen mai da ake hakowa, ba su iya mu kira kan mu kasa mai arzikin danyen man fetur, kama Saudi Arebiya.

Ta ci gaba da cewa karancin kudaden shigar da kasa ke samu ne ya sa tilas sai ta rika ciwo bashi idan za ta gudanar da wasu manyan ayyukan inganta rayuwar jama’a.

A karshen Disamba, 2017 dai bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 21.73.

Idan ba a manta ba dai a cikin satin da ya gabata farashin mai ya karu, har ta kai jama’a na murna.

Sai dai kuma jawabin na Onoha ya sare wa da dama guiwa, jin cewa kasafin kudin 2018 ba zai cimma nasara ba, har sai Najeriya ta ciwo bashi tukunna.

Share.

game da Author