Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya soki gwamnatocin baya cewa sune suka yi raba-raba da kasar nan ya sa aka shiga halin kakanikayi.
Shugaban Buhari ya bada misali kan irin miliyoyin dalolin da aka rinka samu a wancan lokacin amma abu kamar randa, an kwashe su tas.
” Ko da muka hau karagar mulki a 2015, da gudu na ruga ofishin gwamnan babban bankin Najeriya, Emiefele, da hula ta a hannu ina tambayar sa ya bani bayani kan halin da asusun ajiyar Najeriya ke ciki. Buda bakin sa ke da wuya ya ko ce mini asusu fa babu komai a ciki, komai ya kare.
” Haka kuma ga bayanai da na iske a kasa cewa wani shugaban kasa da ya shude wai ya kashe dala biliyan 15 don samr wa kasar nan wutan lantarki, saboda Allah ina wutan yake, Ina tambayan ku ina wutan yake.
” Ba a taba samun cinikin danyen mai ba tun kamar yadda aka samu a gwamnatocin baya amma abin kamar azal, sun kwashe kudin sannan basu yi wa mutanen kasa komai ba.
” Ban damu da abin da zaku ce game da marigayi Abacha ba, abinda zan ce a nan shine na amince in yi aiki dashi kuma a dalilin haka mun gina hanyoyin a ko ina a kasar nan.
Shugaba Buhari ya shaida wa bakin sa ‘yan kungiyar BSO cewa dole ne fa kowa ya maida hankalin sa a taru a ceto Najeriya daga halin da ta shiga.
Ya yaba wa kungiyar cewa Allah ne zai saka musu kan kokarin da take yi da kauna da take nuna masa tun da aka kafa ta.