Wasu ‘yan baranda sun farwa gidan kwamishinan matasa da wasanni na jihar Zamfara, Abdullahi Gurbin Bore a kauyen Gurbin Bore dake jihar in da suka yi garuwa da matarsa da ya’yan sa 6.
Kwamishina Abdullahi ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin labari da wannan abin takaici inda ya bayyana cewa, maharan sun far wa gidan sa ne da karfe 1:30 na daren Talata.
Ya ce an sace matan sa daya, ‘ya’yan sa uku da wasu yan’uwan sa uku da ke zama da iyalan sa, sannan har yanzu masu garkuwan ba su tuntube shi ba.
Discussion about this post