Rahotanni sun tabbatar da kisan mutane 10 a cikin kauyukan Karamar Hukumar Birnin Gwari.
Kisan ya biyo bayan hare-haren da aka kai a kauyukan cikin kwanakin nan biyu.
Maharan da har yau ba a gano su ba, sun dira kauyukan Mashigi, Dakwaro, Sabon Gida da kuma wani kauye inda suka kashe mutane 10.
Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan, mai suna Malam Umar, wanda kuma ya ke cikin wata kungiyar sa-ido kan tsaro a Birnin Gwari, ya shaida cewa an tabbatar da gano gwarwakin mutane 10, amma ya tabbatar akwai wasu kashe-kashen wadanda ba a lissafa da su ba.
Ya ce maharan sun dirar wa kauyukan da misalin karfe 5 na yamma shekaranjiya Talata, kuma sai da suka shafe awa uku da rabi a cikin kauyukan.
Maharan sun banka wa gidaje da rumbunan hatsi wuta kafin su bar kauyukan.
Jami’an tsaro sun tabbatar wa Premium Times kai harin, amma sun kasa yin wani karin bayani.