Ali Modu Sheriff ya yi ganawar Sirri da shugaba Buhari

0

Tsohon gwamnan jihar Barno, Sanata Ali Modu sheriff ya yi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da yammman Alhamis.

Ali Sheriff dai ya fice daga fadar shugaban kasa ne ba tare da ya ce wa manema labari komai ba.

Idan ba a manta ba, Ali Sheriff ya canza sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC bayan batakashi da suka gurza da yan jam’iyyar PDP a lokacin da yake shugabancin ta.

Share.

game da Author