Rundunar sojin Najeriya ta sanar cewa dakarun ta sun kashe ‘yan Boko Haram 15 sannan sun ceto mutane sama da 40 a wani mabuyar su dake kudancin tafkin Chadi.
Kakakin rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ Oneyma Nwachukwu ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba.
Nwachukwu ya bayyana cewa dakarun sojojin sun far wa kudancin tafkin Chadi ne domin fatattakar sauran ragowar ‘yan Boko Haram da suke boye a wasu lunguna a wannan daji.
Ya ce sun kashe ‘yan Boko Haram 11 a kauyen Gomara dake kudancin tafkin Chadi sannan 4 a arewacin jihar Barno.
” Mun kwato makamai hudu, babura hudu, keke NAPEP biyu, mashinan ban ruwa biyu,janareto biyu, rigunan sojoji biyu, na’urar daukan hoto daya da jakan magani daya.”
” Bayan haka mun ceto mata 33, yara 16 duk a mabuyar na su suna sansanin ‘yan gudun hijira a Barno.