Kotu a Kaduna ta daure wani mutum da yayi wa ‘yar shekara 12 fyade

0

Kotun Majistare dake titin Daura, Kaduna ta daure wani mutumi Mai suna Patrick Ben mazaunin Maraban Rido da matar sa ta rasu bayan ta kama shi da laifin yi wa wata yarinya yar shekara 12 fyade.

Nyimze Hinga, da ya shigar da kara ya ce wani mutumin kwarai ne ya sanar masa cewa Patrick ya boye yarinya a dakinsa ne har na tsawon kwanaki 7 sannan iyayenta na ta neman ta.

Alkalin kotun Naheed Ibrahim ya bayyana cewa kotu zata yanke hukuncin wannan kara ne Idan ta kammala samun bayanai akai sannan za ta ci gaba da shari’ar ne a watan gobe.

Shi dai Patrick Ben ya amsa laifin sa a gaban alkali.

Share.

game da Author