Kungiya mai zaman kanta mai suna ‘MedShare’ dake kasar Amurka ta bayyana cewa ta kashe dala miliyan 40 a cikin shekaru 20 da suka wuce don tallafa wa fannin kiwon lafiya a Najeriya.
Mataimakiyar shugaban kungiyar Nell Diallo ta sanar da haka a taron cika shekaru 20 da kungiyar ta yi tana aiki a Najeriya.
” Mun tallafa wa fannin kiwon lafiya a Najeriya da magunguna da kayan aiki da ya kai dala miliyan 40 musamman wanda ya shafi inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana.”
” Mun kuma zage damtse wajen bunkasa aiyuka a manyan asibitocin dake jihohi 19 dake kasar nan.
A karshe shugaban kungiyar ya bayyana a farin cikin sa ga goyon bayan da Kungiyar ke daga Najeriya.
Ya kuma tabbatar da cewa Medshare zata ci gaba da tallafa wa Najeriya da kuma sauran kasashen duniya.