Babban Jami’in kiwon lafiya na jihar Adamawa Batulu Mohammed ya sanar cewa cutar zazzabin lassa ta bullo a jihar.
Ya sanar da haka ne a yau Litini da yake bayanin yadda jami’an Kiwon Lafiya suka gano cutar a jikin wani Gabriel Ambe.
Ya ce Ambe ya rasu sanadiyyar kamuwa da cutar.
Sai dai kuma ya fadi cewa gwamnatin Jihar ta yi maza maza wajen tattaro masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya na Jihar cikin shugabancin kwamishinan kiwon lafiya na jihar Hajiya Binta Atiku Abubakar domin tattaunawa da samar da hanyoyin da za a bi don ganin cutar bata yadu a Jihar ba.