Majalisar Tarayya za ta binciki yadda aka yi wala-wala da naira biliyan 2 da wata dala miliyan 3.8 a Hukumar Wutar Lantarki

0

Yayin da aka rika canja wa Hukumar Samar da Hasken Lantarki suna, inda da farko daga NEPA zuwa PHCN, hakan bai sa ta biya bukatar da ake ta gaganiyar ganin ta biya ba, sai ma kara afkawa cikin harkalla da wawuran kudade hukumar ta kara yi.

Dalili kenan ma Majalisar Tarayya a yau ta bayar da umarnin kafa kwamiti wanda zai binciki wata wala-wala har ta naira biliyan biyu da kuma ta dala miliyan 3.8 da aka yi da kudaden da aka saida hukumar PHCN ga ‘yan kasuwa masu zaman kan su.

Wannan umarnin kafa kwamiti ya fito ne daga sanadiyyar wani kudiri da Hon. Chukwuka Onyema na jihar Anabra ya kawo a zaman majalisar na yau Talata.

Majalisar ta yanke shawarar kafa kwamitin ne wanda zai binciki salwantar kudaden kuma ya mika rahoton sa a cikin makonni shida.

Onyema ya ce sakamakon gyaran Tsarin Samar da Hasken Lantarki na 2005, an karkasa PHCN zuwa gida 18, ya ce an sayar wa wadannan kamfanoni ne su kuma suka rika raba ta a jihohi daban-daban aka roka kiran su LEDC.

Dan Majalisar ya ce wadannan kamfanoni sun rika biyan kudaden ruwa ta wani asusu na bankin Standard Charted Bank, Fedility Bank, Stanbic IBTC, Access Bank, Sky Bank, Sterling Bank, Zenith Bank da kuma Unity Bank.

Ya ci gaba da cewa an tara wa gwamnatin tarayya kudin ruwa har naira bilyan biyu da kuma wata dala milyan 3.8, amma ba a san yadda aka yi da it aba.

Don haka ya ce Majalisar Tarayya na da hakkin binciken yadda aka yi da wadannan kudade.

Share.

game da Author