Yadda mu ke karfafa hanyoyin samun bayanai na sirri -Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ta maida hankali sosai wajen ingantawa da karfafa hanyoyin da ta ke bi wajen samun bayanai na sirri a cikin kasa, da nufin kakkabe hare-haren ta’addanci da kuma sauran muggan laifuka a cikin kasar nan.

Buhari yayi wannan jawabi ne a yau Talata a Taron Shakara-shekara na takwas a kan Tsaron Kasa, wanda tsoffin daliban Kwalejin Tsaro ta Kasa kan shirya duk shekara, a Abuja.

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya wakilci shugaba Buhari a wurin taron.

Ya ci gaba da cewa akwai iyakar gejin ci gaban da za a iya samu ta hanyar yadda jami’an tsaro za su iya samarwa ta hanyar gina barikoki da sansanoni.

“Daya daga cikin hanyoyin da a yanzu mu ke bi mu na samun bayanai na sirri shi ne tabbatar da cewa hanyar samun bayanai na sirri ba harka ce ta jami’an tsaro su kadai ba. Ya ce harka ce da ta shafi daukacin kowace al’umma bai daya.

Buhari ya furta a ta bakin mataimakin sa bakin sa, yaki da Boko Haram abu ne a yanzu da ya fadada saboda fadin yankin Arewa-maso-gabas.

Share.

game da Author