Jami’ar gwamnatin tarayya dake Gusau jihar Zamfara ta sallami wasu daliban makarantar su 15 saboda rashin maida hankali ga karatun su.
Shugaban jami’ar Magaji Garba ya sanar da haka a taron yaye daliban makarantar da aka yi ranar Laraba a Gusau sannan ya kara da cewa hakan ya zama dole ganin yadda daliban suka ki maida hankali kan da karatun su.
” Daga yanzu za mu kori duk dalibin da sakamakon jarabawar sa bai wuce 1.0 daga makarantan nan.”
Discussion about this post