RIKICIN KASUWAR MAGANI: Gwamnatin Kaduna ta gurfanar da mutane 63 a kotu

0

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya umurci jami’an tsaron jihar da su taso masa keyar wadanda suka tada rikicin Kasuwar Magani dake Kajuru, jihar Kaduna.

Gwamnatin jihar Kaduna ta maka wasu mutane 63 da take zargin su da hannun dumu-dumu a tada rikicin,
Rikicin yayi ajalin mutane 12 sannan anyi asarar dukiyoyi masu dimbin yawa.

Babban Sakataren ma’aikatan shari’a na jihar, Chris Umaru ya tsokata wa manema labarai cewa an gurfanar da mutanan ne a kotun dake lamba 6 a titin Daura, Kaduna.

Bayan haka kotun ta daga zaman ta zuwa ranar 15 ga watan Maris domin ci gaba da shari’ar, sannan ta bada umurnin a ci gaba da daure mutanen kurkuku zuwa wannan rana.

Mai ba gwamnan Kaduna shawara kan harkar siyasa da ayyukan gwamnati, Uba Sani ya ziyarci Kasuwar magani domin yin ziyara gani wa Ido irin hasarar da mazaunan yankin suka yi sanadiyyar rikici da ya barke a Kasuwar.

Uba da tawagar sa sun ziyarci Kasuwar ne ranar Alhamis din da ya gabata, inda suka gana da mazauna yankin sannan suka duba irin taimako da gudunmuwar da za su iya kaiwa mutanen yankin.

” Na yi wannan ziyara ne domin in duba ku sannan in taya gwamnati rokon ku da mu zauna lafiya a tsakanin juna. Ina mai tabbatar muku da cewa gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin gwamna Nasir El-Rufai za ta yi duk abinda za tayi domin ganin irin haka bai sake faruwa.

Share.

game da Author