Masana da dama na hanyen cewa dawowar da Boko Haram suka yi su na kai hare-hare a yankin Arewa maso gabas, ya ta’allaka ne da irin shirmen da gwamnatin Najeriya ta tabka. Haka wasu masana harkokin tsaro su ka bayyana wa PREMIUM TIMES.
Sun bayyana cewa irin matakan da gwamnati ke dauka a yanzu ne ke taimaka wa ‘yan ta’adda su na samun karfin da har su ke kawo wa sojoji cikas.
Ganin yadda a gefe daya gwamnati ke cewa ta gama da Boko Haram kwata-kwata, su kuma Boko Haram su ke kara kaimin kawo hare-hare har suka sace dalibai mata a sakandaren Dapchi, sai PREMIUM TIMES ta nemi jin ra’ayoyin masana harkokin tsaro daban-daban.
Sun hakkake cewa wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin gwamnati da Boko Haram, ba ta zama alheri ga kokarin da ake yi na magance Boko Haram ba.
Ra’ayin wadannan masana ya tafi a kan cewa makudan kudade gwamnati ta bai wa Boko Haram, kuma ta saki wasu kwamandojin kungiyar sannan aka saki daliban Chibok 107 da kuma matan nan 10 da aka tsare da kuma malaman Jami’ar Maiduguri uku da sako kwanan nan, babban kuskure ne.
Duk da har yau ita gwamnatin tarayya ba ta fito ta ce ta bayar da kudi kafin a sallami daliban Chibok da masu neman danyen man fetur ba.
PREMIUM TIMES ta ruwaito kuma ta buga a kwanan baya yadda wasu Sanatocin suka ambaci cewa sai da aka bayar da kudi kafin a sallami wadanda ka yi garkuwar da su.
HARE-HAREN BAYA BAYAN NAN
Cikin makonnin da suka gabata, Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare cikin jihohin Barno da Yobe, har abin ya kai ga satar daliban #Dapchi da kuma kashe wasu jami’ai masu yi wa Majalisar Dinkin Duniya aiki.
Sai dai kuma duk da wadannan munanan hare-hare, Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya tsaya kai da fata cewa an kakkabe Boko Haram. Kawai dai za a iya cewa sun kai harin sace daliban Dapchi domin su samu kafafen yada labarai su rika yayata su.
Kwanaki 11 daidai bayan kai harin satar dalibai a #Dapchi, sai Boko Haram suka kai wani mummunan farmaki a garin Rann, hedikwatar karamar hukumar Kala-Balge a jihar Barno, suka kashe mutane 11, ciki har da ma’aikatan majalisar dinkin duniya su uku, sai kuma jami’an tsaron Najeriya takwas.
Washegari da dare kuma, sai maharan nan su ka kai wani sabon hari a karamar hukumar Madagali cikin jihar Adamawa, suka arce da mutane uku.
Ranar Litinin kuma wani dan kunar-bakin-wake shi kadai, ya kai hari a Maiduguri, inda ya kashe jami’an tsaro na CJTF su uku, ya raunata wasu 17.
Dalili kenan masana harkokin tsaro suka rika yin Allah-wadai da wannan tsari na bada kudade ko mika kwamandojin Boko Haram ana yin musaya da wadanda suka sace, suka tsare.
Har ila yau kuma su na ganin babban kuskure ne yadda Najeriya ke sakin wasu ‘yan Boko Haram, ana cewa sun tuba, za su je su gyara halayen su.
Baya-bayan nan dai an saki wasu har su 400 da ake tsare da su a barikin sojoji na Kainji.
Daya daga cikin wadanda aka yi hira da su, shi ne Ahmed Abdullahi, wanda shi ne tsohon Daraktan Jami’an Tsaro na DSS a jihar Borno, har tsawon shekara shida.
Abdullahi wanda ya bar aiki cikin 2015, ya ce maganar gaskiya babban kuskure ne da kuma batan-hanya a ce gwamnati na tattaunawa da Boko Haram a lokacin da ake cikin yaki da su.
Abdullahi, wanda shi ne ya assasa kafa CJTF, kuma ya sha fita farmakin kama manyan gogarmomin Boko Haram, ya ce wasu lokutan har kuka ya ke yi idan ya tuna irin kokarin da suka yi cikin shekaru, amma a yanzu wadanda ke gudanar da harkar tsaro na warware hancin tubkar da suka yi.
“To wai a haka ne za a yi nasara kan yaki da Boko Haram din? Kusan dukkan rikakkun ‘yan ta’addar da muka sha wahala, muka sadaukar da kan mu muka kamo, duk an kwashe su, an bayar da su musanya don a sako daliban Chibok.”
Sai ya kara da cewa sace daliban #Dapchi da Boko Haram suka yi, wata hanya ce kawai da suka ga ita za su bi domin su kara samun tulin kudaden daloli da Yuro.
Discussion about this post