Dalilin da ya sa ake yawan kashe ‘yan Najeriya a Afrika ta Kudu

0

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana cewa yawancin kisan da ake wa ‘yan Najeriya a Afrika ta kudu, ba kabilanci ba ne, ba kuma kiyayyar jinsi bace, kawai kisan gilla ne.

Kakakin Ma’aikatar, Tope Elias-F atile, ta bayyna haka yayin da ya ke yi wa kafafen yada labarai jawabi dangane da yadda ma’aikatar ke gudanar da sha’anin ta.

Ya ce Ma’aikatar Harkokin Waje na yawan tuntubar shugabannin kungiyoyin ‘yan Najeriya mazauna Afrika.

Ana yawan samun rahotonnin da ke bayyana ana kashe ‘yan Naijeriya a Afrika Ta Kudu,. Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa a cikin shekara biyu an yi wa ‘yan Nijeriya 20 kisan-rubdugu a Afrika ta Kudu.

Share.

game da Author