Hukumar Raba Man Fetur, wadda ke karkashin NNPC, wato DPR, ta bayyana cewa ta ciki tarar wasu manyan dillalan fetur 20 tara wadda ta kai naira biliyan 2.5.
Daraktan hukumar Dordecain Ladan, ne ya bayyana haka a taron da shugabannin shiyyoyi suka gabatar a Abuja ranar Talatar da ta gabata.
Shugaban Hulda da Jama’a na DPR, Saidu Bulama, ya shaida wa ‘yan jarida cewa manyan dillalan fetur din sun yi kokarin yadda za a yi ba a bankado su ba, saboda sun tabka harkallar karkatar da fetur din ne tsakanin 9 Ga Disamba, 2017 zuwa 3 Ga Fabrairu, 2018.
Ya ce tsakanin Janairu da Fabrairu kuma, sun gano cewa masu gidajen mai sun karkatar da tanka har 162, wanda adadin ya haura lita milyan tara kenan.
Ya ce a Kano kadai wani babban dan bumburutu ya karkatar da tirela 115 shi kadai, wadda aka kwashi man ne daga daffo na NNPC da ke Kano.
Ya ce wanda ya an ci tarar wanda ya karkatar da mai daga Kano, zai biya naira 275 a kowace lita daya da ya karkatar, maimakon 145. Wato adadin naira biliyan 1.2 aka ci shi tara kenan shi kadai.
Ya ce sauran wadanda aka ci tarar sunn farac kawo rasidai dominnsu nuna cewa sunn zuba kudin ntarar a Asusun Bai Daya na Gwamnatin Tarayya.