Kusan watanni hudu kenan tun bayan damka wa Shugaba Muhammadu Buhari rahoton kwamacalar mayar da Abdulrashid Maina kan aiki, amma har yau ya yi kemadagas, bai ce komai ba.
Masu sukar irin takun mulkin Buhari sun ce, ya na ta walle-walle da rahoton ne, har ‘yan Najeriya su manta da abin.
Sai dai kuma magoya bayan sa a masu ra’ayin cewa Buhari bai yi watsi da batun Maina ba. Shi mutum ne wanda sai ya tantace gaskiyar Abu sannan sai zai dauki mataki a kan sa. Sun ce don haka shi ya say a ke lallabawa a kan komai.
A cikin wani shirin sunkuru ne dai aka maida Abdulrashid Maina kan aiki, a cikin watan Satumba, 2017, bayan shekara hudu da korar sa daga aiki a bisa zargin karkatar da makudan kudaden fansho.
Annkore shi ne a lokacin muklin Goodluck Jonathan, maimakon ya tsaya yak are kan sa, sai ya sulale ya bar kasar, bayan da jami’an EFCC suka nemi damke shi.
Tun daga lokacin ba a cika ganin sa, sai dai jin sa, har sai cikin watan Oktoba, 2017, lokacin da PREMIUM TIMES Ta fallasa cewa gwamnatin Buhari ta maida Maina kan aikin sa.
To sai dai kuma bayan da aka rika ragargazar gwamnatin Buhari, sai ya bada umarnin cewa a sallame shi kuma a binciki batun. Ya kuma nemi a kawo masa kwafen bayanan yadda aka yi aka cusa shi cikin ma’aikata.
An yi ta jifar juna da duwatsun alhakin maida Maina kan aiki, a tsakanin shugabar ma’aikata, Winnifred Oyo-Ita, Ministan Shari’a Abubakar Malami, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari.
Discussion about this post