An gurfanar da wata da ta gartsa wa wani jami’an wutar lantarki cizo

0

Wata mata mai shekaru 28, mai suna Kemi Shopade, ta gurfana a gaban alkali, a bisa tuhumar ta da ake yi ta gartsa wa wasu jami’an kamfanin wutar lantarki cizo.

Shopade, ta cic-cije su ne a lokacin da suke kokarin yanke wayar wutar gidan ta, a Lagos.

An gurfanar da ita ne a yau Laraba a Kotun Majistare ta Ikeja, Lagos.

Ana tuhumar Shopade wadda ke zaune a Alaguntan da ke cikin unguwar Iyana-Ipaje, Lagos da laifin hada baki da wasu biyu suka nuna wa ma’aikatan hukumar hasken lantarki fin karfi, har suka ji musu ciwo ta hanyar cizo.
Mai gabatar da kara, Godwin Awuse, ya ce wadanda ake zargin sun aikata laifin ne tun a ranar 24 Ga Nuwamba, 2017 a gidan ta.

Awuse ya ce wadda ake zargin sun yi wa ma’aikatan taron-dangi ne su ka ji musu ciwo. Ya ce sauran biyun wato Oluwole Johnson, da Ibiam Uwaoman ba kai ga kama su ba, tukunna, amma za su kamo su.

Ya ce jami’an sun yanke mata wuta ne domin rabon da ta biya kudin wuta, tun cikin Janairu, 2017, shekara daya kenan.

Za a ci gaba da shari’a ranar 5 Ga Janairu, 2018.

Share.

game da Author