Ba a yi watandar gidaje 222 ba, inji EFCC

0

Hukumar EFCC ta musanta ikirarin da kwamitin Majalisar Tarayya ya yi a jiya cewa wai sun karkatar da gidaje 222 da Maina ya kwato tare da yin watandar su a tsakanin su.

EFCC ta ce wadannan gidaje da ake magana akai, babu ko daya a hannun ta.

Wannan raddi ya biyo bayan furucin da Sanata Emmanuel Paulker, Shugaban Kwamitin binciken yadda aka yi satar-hanya aka maida Abdulrashid Maina aikin sa.

A wata takardar bayanai da kakakin yada labaran EFCC, Wilson Awujeren, ya karyata Sanatan ya na mai cewa har yau
“Ganin yadda wasu jama’a ke ta yawan nuna jahilci da rashi dangane da kadarorin da aka kakkarbo, ina son na jaddada cewa ba zai yiwu wani ko da wasu su kwashi kadarorin nan su said a ko su raba a junan su ba.Yawanci maganar kudaden fatana kotu.”

“Mu na son mu cire wani tunani ko kokwanto a zukatan jama’a cewa babu wasu gidaje 222 a ko’ina dawai aka raba takanin wasu.

“EFCC na sanar da cewa duk wasu kadarori da aka kwato daga wadanda suka saci kudaden fansho na ‘yan sanda da na Ofishin Fansho na Ofishin Shugaban Ma’aikata, duk an sanar da hukumomin da ya kamata a sanar da su na gwamnati.

“Daga cikin kadarorin da ka kwato a wurin barayin kudaden fansho, in banda kadarorin da John Yusuf ya bayar domin a yi masa sassauci, wadanda aka damka wa gwamnatin tarayya, banda Brifina Hotel, duk sauran ana kan tirka-tirkar shari’a kan su a kotu.”

Share.

game da Author