Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta tasa keyar wata mata mai suna Roseline Micheal bayan an kamata da laifin yayyanka yar kishiya mai shekaru takwas da sabuwar reza don wai sun yi fada da yar cikin ta.
Mahaifin yarinyar ya ce matar sa ta Kira sa a waya cewa za ta rama wa ‘yar ta dukan da yar kishiya tayi mata.” Daga nan nayi ta rokon ta Kada ta aikata wani abu da zata yi da na sani ba, ta ko ki ji.
Yanzu dai yarinyar na kwance a asibiti ana duba ta.
Roseline ta ce ta bi hudubar shaidan ne amma tayi nadamar abin da tayi.
Yanzu dai rundunar ‘yan sanda ta kai Roseline kotun karen hakkin yara na jihar.