Gwamnatin Tarayya ta raba zunzurutin kudi har naira biliyan 80 domin rage wa ‘yan Najeriya radadin talauci.
Kudin dai an raba su ne a karkashin shirin bayar da tallafi na Social Intervention Programmes, wato SIP.
Wannan bayani ya fito ne a wurin kaddamar da wani littafi wanda a cikin sa aka yi bita da nazarin shekaru biyu na gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Littafin dai gamayyar jami’ai da hadiman da ke kula da harkokin yada labaran shugaban kasa ne suka hadu suka wallafa shi.
Sun bayyyana cewa kimanin naira biliyan 500 aka yi kintacen kashewa a cikin shekarar 2016. “Amma a zuwa yanzu an damka naira bilyan 80 ga jami’in kula da kudaden tsare-tsaren na SIPs, a Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare-tsare, tun a farkon watanni uku na karshen shekarar nan.
” Dalili ke nan a ke ganin ana ta gudanar da wasu tsare-tsare a kwanan nan.”
Wasu daga cikin irin wadannan tsare-tsaren rage radadin fatara da talauci a cikin al’umma, wato SIPs, sun hada shirin N-Power, wanda shi dama shiri ne hususan don taimaka wa matasa su iya kasuwanci ko kuma a ce sana’o’in da za su dogara da su han da shekaru masu yawa.
Baya ga shirin N-POWER, wani bangare da ake kashe kudaden tallafin kuma su ne ta hanya ciyar da dalibai ‘yan firamare a kasar nan.
Sauran kuma sun hada kudaden tallafi ga masu karamin karfi da kuma shirin taimakawa masu kananan sana’o’i da jari.
Littafin dai ya kunshi shafuka 348 da ya kunshi ci gaban da Ma’aikatu suka yi karkashin Ministocin su da kuma nasarorin wasu daidaikun hukumomi na gwamnatin tarayya.
Za a kaddamar da littafin ranar 16 ga Nuwamba. Bola Tinubu zai kaddamar da shi, yayin da Tony Momoh zai yi sharhin littafin.