Wani lauya mai aikin kare hakkin jama’a, Jiti Ogunye ya yi karin hasken yadda gwamnatin Jihar Kaduna za ta kori malaman firamare 21,780 a bisa sharuddan doka.
Lauya Ogunye ya ce malaman wadanda suka kasa cin jarabawar ‘yan firamare, ya ce kada a kore su, sai dai kididdige su a kirkiro wasu hanyoyi da za a rabu da su salum-alum.
Wannan jarabawar da malaman suka fadi dai ta jawo musu ka-na-ce yayin da kowa ke tofa albarkacin bakinsa.
Amsoshin da su ka bayar sun nuna irin matsalar da ke tattare da aikin da karancin ilimi da malaman me fama da su.
Kashi 2/3 na malaman sun kasa cin maki 75, abin da ya janyo ‘yan Najeriya ke ta nuna damuwa a kan halin da ilimi ke ciki a kasar.
Ita dai gwamnatin jihar Kaduna ta sha alwashin sallamar malaman, yayin da kungiyar malamai ta jihar tuni ta tashi ta na kartar kasa.
Sannan kuma gwamnatin jihar ta ce za ta dauki wasu har har 25,000, amma kwararru wadanda za su maye gurabun wadancan.
To sai dai shi lauya Ogunye, ya ce matsalar rashin kwarewar wadanda za a korar, ta samo asali ne daga ita kanta gwamnati da kuma tsarin ilimin da Najeriya ke a kai, inda ya ce abu ne da ya wajaba kasar nan gaba daya a tashi tsaye don shawo kan sa.
Ya kara da cewa: “Malamai da Kungiyar Kwadago da sauran masu fada da El-Rufai a kan matsalar malaman su na yi ne don wani dalili na kashin kan su kawai.”
Ya kara da cewa a gaskiya jinjina ya kamata a yi wa gwamnan ba tsangwama ba. Ya ce duk irin yadda ilimi ya lalace a manyan makarantu, to ya na da nasaba da rokon sakainar kashi da Jihohin da ba su maida hankali kan inganta ilimin ba ne.
Ya ce tun shekaru da dama Jihohin Arewa su ka yi watsi da tsarin yi wa malamai gwaji na TDNA, to sai ga shi yau El-Rufai ya taro wannan matsala kan sa a tsaye.
A kan haka ne ya ce kamata ya yi a bai wa wadannan malamai horon da ya kamata, domin a kara zakulo wadanda za a iya tafiya tare da su.
Discussion about this post