Dan bindiga ya bude wuta a Fadar Sarkin Saudiyya

0

Jiya Asabar ne wani matashin dan bindiga ya kai hari a Fadar Salman, Sarkin Saudiyya, da ke Jedda.

Kamfanin Dillanacin Labarai na Saudi Press ya ruwaito Ministan Cikin Gidan kasar na cewa wanda ya kai harin ya kashe mutane buyu kuma ya jikkata uku.

An bayyana cewa haifaffen kasar ta Saudiyya ne mai shekaru kimanin 28.

Zaratan Dogaran Tsaron Fadar Sarkin sun bude masa wuta, inda su ka kashe shi tun a bakin kofar shiga fadar.

Share.

game da Author