Wasu masana kuma likitoci sun yi kira ga gwamnatin Najeriya kan ingancin wayar da kan mutanen kasar game da cutar daji domin rage yaduwar ta.
Masanan sun yi wannan kira ne a taron samarda da mafita kan yaduwar cutar daji da aka yi a Abuja.
Masanan sun ce Najeriya za ta iya rage yaduwar cutar idan mutane musamman mazauna karkara su sami sani game da yadda za su iya guje wa kamuwa da cutar.
Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa a taron jami’in babbar bakin duniya Olumide Okunola yace bincike ya nuna cewa mutane 250,000 ne ke kamuwa da cutar daji kowani shekara a Najeriya sannan 100,000 daga cikinsu na rasa rayukansu sanadiyyar haka.
Ya ce banda haka kadan daga cikin mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya ne kadai ke samun magani wanda a asibitocin kasashen waje ne ma domin asibitocin kasar duk sun lalace.
Saboda hakan ne Olumide Okunola ya yi kira ga gwamantin tarayya da ta ware isassun kudade domin bunkasa fannin kula da mutanen da suka kamu da cutar daji, ta dauki kwararrun ma’aikatan da za su kula da wadanda suka kamu da cutar hadi da samar da kayayyakin aiki a asibitocin.