Sama da yara 140 ne suka kamu da cutar Kenda a jihar Kwara

0

Wani jami’in kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO Wole Adaramola ya sanar da cewa tsakain watannin tara da suka wuce mutane 147 ne suka kamu da cutar kenda a jihar Kwara.

Ya sanar da hakan ne a taron sanin Makamashi aiki na ma’aikatan kiwon lafiya da aka yi a Ilorin domin hana yaduwar cutar.

‘‘Tsakanin watannin Janairu zuwa Agusta mutane 147 daga kananan hukumomi 16 a jihar Kwara suka kamu da cutar na kenda.”

Ya ce a kwanakin baya jihar Kwara ta yi wa kashi 76.4 bisa 100 na yara kanana alluran rigakafin cutar amma yanzu hakan muna sa ran yi wa kowani yaro rigakafin cutar a jihar.

Wole Adaramola ya ce kungiyar WHO za ta hada guiwa da hukumar UNICEF,hukumar PHCDA na jihar Kwara da masu ruwa da tsakin a harkar kiwon lafiya a jihar domin ganin ta cin ma burinta.

Daga karshe shugaban hukumar PHCDA na jihar Abimbola Olorunfunso ta ce rashin yi wa yara alluran rigakafin ne ke dawo da cutar kenda a jihar.

Ta yi kira ga iyaye da su tabbatar sun yi wa yaransu alluran rigakafin cutar don hakan zai taimaka wajen kare yaran su daga cutar.

Share.

game da Author